Sanata Ali Ndume, yace mayakan Boko Haram sun kashe mutane fiye da 300 a jihar Borno sakamakon hare haren da suka kai sau 252 cikin watanni 6 da suka shude, wanda hakan ya tilasta gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, zuwa birnin tarayya Abuja don tattaunawa da manyan hafsoshin tsaro akan yadda za’a magance matsalolin ƙaruwar ayyukan Boko Haram a jihar sa.
Ndume, ya bayyana hakan a jiya Lahadi lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Sanatan wanda ke cikin tawagar da ta ziyarci babban hafsan tsaron ƙasa Janar Christopher Musa, da hafsan sojin kasa, da takwaran sa na rundunar soji sama da na ruwa a Abuja, ya bayyana cewa sojojin na yin iya kokarinsu.
Ndume, yace dalilin ziyarar shine su tattauna da manyan jami’an tsaron akan dawowar ayyukan Boko Haram a jihar Borno, saboda a cewar sa daga watan Nuwamba na shekarar 2024 zuwa yau mayakan sun kai hari 252, wanda hakan yayi sanadiyar kashe sojoji fiye da 100, da kisan fararen hula fiye da 200.