Gwamnatin tarayya zata fara cin ƴan kasashen waje tara akan ƙin komawa kasashen su

0
51

Gwamnatin tarayya ta sanar da wasu sabbin dokokin da suka shafi samar da takardun izinin shigo wa Najeriya ga ƴan ƙasashen waje, inda ta yi gargaɗin cewa masu karya dokar za su iya fuskantar haramcin sake samun damar shigowa ƙasar har na tsawon shekara 10.

Wannan matakin dai zai soma aiki nan da watan gobe na Mayu.

A cewar ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, za a tabbatar da an tantance waɗanda za su shigo Najeriya tare da cin waɗanda bizar su ta ƙare amma ba su sabunta ba tarar dala 15 kowace rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here