Gwamnatin jihar Lagos ta sanar da cewa zats fara ɗaure direbobi masu shan sigari da ciye-ciye a lokacin tuƙi.
Hukumar kiyaye cunkoson ababen hawa ta jihar Lagos LASTMA, ce ta yi gargadin hakan, tana mai cewa hukuncin da za’a riƙa yanke wa masu ciye-ciye ko shaye shayen abubuwa yayin da suke tsaka da tuki ya ƙunshi kwace abin hawa, rufe matuƙi a gidan gyaran hali tsawon watanni 3, ko kuma yin aiki ga al’umma na tsawon watanni 6.
LASTMA, tace an samar da wannan doka domin kiyaye daukewar hankali ga direbobi yayin da suke tsaka da tuƙi, da kuma hana afkuwar haɗari.