Bello Turji ya kashe manoma a jihar Sokoto

0
74

Ƙasurgumin dan ta’adda Bello Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu dake Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.

Bashiru Altine Guyawa, mai bibiyar lamarin rashin tsaro a yankin Sokoto ya bayyanawa manema labarai cewa, Turji ya kashe mutanen a lokacin da ya dawo daga yawon sallah.

Yace Turji da yaran sa sun bar kauyen Fakai a Karamar Hukumar Shinkafi inda suka shiga wasu kauyuka a Karamar Hukumar Isa, sannan a hanyarsu ta komawa Fakai bayan gama yawon Sallah suka kashe manoma 11.

A lokacin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i ya ce, jami’an soja ne kadai za su iya tabbatar da farmakin saboda su ne ke aiki a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here