An gano wajen da ake haɗa makamai a jihar Kano

0
109

Rundunar ƴan sandan ta ƙasa ta bayyana cewa gano wani waje da ɓata gari suke amfani dashi don haɗa makamai a jihar Kano.

Rundunar tace ta kama wasu mutum uku da kwato bindigogi 15 kirar gida da harsashi 102, a wajen.

Waɗanda ake zargi da aikata lefin haɗa makaman sun haɗar da Abdul Sadiq ɗan shekara 43 da Ahmad Mu’azu mai shekaru 22, sai kuma Aliyu Sharif, mai shekaru 40.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan ta ƙasa, Olumuyiwa Adejobi, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Yace jami’an su sun samu nasarar kama waɗanda ake zargin a ranar 10 ga watan Afrilu a unguwar Dorayi Babba bayan samun sahihan bayanai da suka kai ga gano tarin haramtattun makaman.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here