Aljeriya ta bai wa jami’an diflomasiyyar Faransa 12 sa’o’i 48 su bar ƙasar, kamar yadda ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya bayyana a yau Litinin, yana mai cewa wannan mataki na da alaƙa da kama ‘yan Aljeriya a Faransa.J
ean-Noel Barrot yayi kira ga hukumomin Aljeriya da su yi watsi da waɗannan matakan korar jami’an, inda yace idan wannan matakin na korar jam’ian su bai sauya ba, ba su da wani zaɓi face mayar da martani kai tsaye.
TRT AFRIKA tace, Jami’an 12 sun haɗa da mambobin ma’aikatar cikin gida ta Faransa, kamar yadda wata majiya ta diflomasiyya ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran AFP.
Ranar Juma’a, masu gabatar da ƙarar Faransa sun tuhumi ‘yan Aljeriya uku, ciki har da wani jami’in jakadanci kan zargin hannu a garkuwa da aka yi da wani shahararren ɗan Aljeriya, Amir Boukhors, a watan Afrilun shekarar 2024 a wata unguwa da ke wajen birnin Paris.
Tuhumar na zuwa ne a wani lokacin da ake zaman ɗar-ɗar tsakanin Aljeriya da tsohuwar uwar gijiyarta, inda Algiers take iƙirarin cewa matakan na da zummar katse ƙoƙarin da ake na gyara dangantakar kasashen biyu.
Boukhors, da aka fi sani da suna “Amir DZ”, wani mai adawa ne da gwamnatin Aljeriya wanda yake da fiye da mabiya miliyan ɗaya a TikTok.
Ya kasance a Faransa tun shekarar 2016 kuma an ba shi mafakar siyasa a shekarar 2023.
An yi garkuwa da shi a watan Afrilun shekarar 2024 kuma an sake shi washe gari, in ji lauyansa.
Algiers na neman mutumin ya dawo ya fuskanci shari’a, bayan an ba da sammacin kamo shi, inda ake zarginsa da laifukan damfara da ta’addanci.