Ƴan ta’adda sun banka wuta a masallacin juma’a da gidaden mutane

0
78

Wasu da ake kyautata zaton ƴan fashin daji ne sun ƙone wani masallacin juma’a na cibiyar kula da lafiya a matakin farko da kuma wasu gidaje fiye da 10 a kauyen Biyabiki dake ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Lamarin ya faru da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar, wanda ake zaton yan bindigar sun kai harin da manufar ɗaukar fansar kisan wani ƙasurgumin ɗan ta’adda wato Adamu Aliero.

Sai dai wata majiya a garin tace har ila yau harin zai iya kasancewa an kai shi saboda kisan wani ɗan uwan Aliero mai suna Isuhu Yellow da ɗansa a makonnin da suka gabata.

Maharan sun kuma kai farmaki ƙauyen Tsageru tare da ƙone gidaje.

Zuwa yanzu dai ba’a ji martani daga rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ba, sakamakon ba’a samu damar jin ta bakin kakakin rundunar ba wato DSP Yazid Abubakar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here