Gwamnatin tarayya ta ce ba ta hana jihohin Arewa Maso Gabas samun cibiyoyi na musamman na sarrafa amfanin gona (SAPZ) ba.
Hakan ya biyo bayan saɓanin koken da ‘yan majalisar tarayya daga yankin suka yi na cewa an hana jihohin su damar shiga shirin.
‘Yan majalisar tarayya daga yankin Arewa Maso Gabas sun yi ƙorafin cewa an nuna wa yankin wariya game da samar da cibiyoyin SAPZ bayan an ƙaddamar da mataki na farko na shirin samar da cibiyoyin na sarrafa amfanin gona a jihar Kaduna ranar 8 ga watan Afrilu.
Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai daga jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da kuma Yobe sun ce ba daidai ba ne a ce babu wata jiha daga Arewa Maso Gabashin ƙasar da ta samu wannan cibiya.
Sai dai Ministan Noma Abubakar Kyari, ya ce ‘yan majalisar sun yi kuskure domin gwamnatin ba ta nuna wa jihohin yankin wariyar hana su cin gajiyar shirin ba.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Abubakar Kyari ya ce jihohin Kaduna da Kano da Kwara da Oyo da Ogun da Imo da Cross River da kuma Birnin Tarayya Abuja su ne suka rubuta takardar neman cibiyoyin kuma suka cika sharuÉ—É—an ba da cibiyoyin tun lokacin da aka fara shirin a shekarar 2019.