Rundunar ‘yan sandan ƙasa ta ce ta sami nasarar kuɓutar da wasu yara ashirin da uku daga wani gidan marayu da ke Unguwar Kubwa a a birnin tarayya Abuja, wanda ake zargin ana fakewa da shi ana hada-hada da safarar yara a cikin Najeriya har zuwa ƙasashen waje.
BBC ta rawaito cewa cikin yaran da aka samu akwai ƴan shekara ɗaya zuwa uku, wasun su kuma suna da kimanin shekara uku a gidan.
DSP Mansir Hassan, shi ne jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ya ce jami’an rundunar sun karaɗe jihohi goma sha ɗaya a ƙoƙarin bankaɗo gidan da ake safarar yaran da kamo wadan da suke da hannu a satar yara, tare da hada hadar siyar da su.