Shugaban hukumar karɓar koke koke da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, yace fiye da mutane dubu 11, sun nemi aikin gurbin mutane 100, da hukumar da zata ɗauka aiki a cikin kwanaki 3 kacal.
Hukumar ta buɗe shafin da za’a yi rijistar neman gurbin aikin a ranar 7 ga watan Afrilu sannan za’a rufe shi a tsakar daren Lahadi.
Muhyi, yace zuwa yammacin ranar Alhamis mutane 10, 757, sun nemi aikin, sannan zuwa karfe 10 na daren ranar mutanen sun kai dubu 11.
Rimingado, ya ɗora alhakin yawan masu neman aikin akan yadda rashin aikin yi yayi ƙamari a tsakanin al’umma.
Yace sun ɗauki matakin bayar da damar neman aikin ta Internet don yin adalci ga kowa.