Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano Abba El-Mustapha ya jaddada aniyar sa ta kawo karshen ayyukan rashin tarbiyyar da ke faruwa a shafukan sada zumunta a Kano.
Ya sanar da hakan a jiya juma’a lokacin da hukumar ta samun nasarar kama wasu matasa biyu yan TikTok da ake zargi da nuna rashin ɗa’a tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Matasan sune Isah Kabir da fatima Adam, wanda kotu ta aike da su gidan gyaran hali na tsawon makonni biyu kafin a dawo domin yanke musu hukunci akan aikata rashin tarbiyya a dandalin sada zumunta.