Gidauniyar ADG ta bayar da tallafin karatu a yankin Kano ta arewa

0
33

Gidauniyar ADG karkashin jagorancin Engr. Rabiu Aliyu Garo ta kaddamar da wani gagarumin rangadi na bayar da tallafi a makarantun sakandire dake kananan hukumomin Kano ta Arewa 13 domin tallafawa dalibai da kayayyakin koyo da koyarwa. 

An fara fara bayar da tallafin da kananan hukumomin Rimin Gado da Kabo, inda aka gudanar da taron karawa juna sani na wayar da kan dalibai akan yadda za su yi karatun gaba da sakandare cikin hikima da tsari. 

Gidauniyar ta kuma biya wa wasu dalibai kudin jarabawar WAEC domin tallafa musu wajen neman ilimi mai zurfi ba tare da cikas ba. 

Bugu da kari, an raba kayayyakin koyon ilimi da kyautuka na musamman ga daliban da suka nuna kwazo da hazaka a makarantun su, wanda hakan ke karfafa gwiwar matasa wajen jajircewa da neman ilimi. 

Engr. Rabiu Aliyu Garo ya jaddada kudirin gidauniyar na ganin kowane dalibi a yankin ya samu ilimi mai inganci tare da tallafi da shawarwari da za su taimaka wajen gina kyakkyawar al’umma.

Ɗaliban da suka amfana da tallafin haɗi da shugabannin makarantun su, sun bayyana farin ciki da godiya akan tallafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here