An sace motar ofishin Nuhu Ribadu a masallacin Juma’a

0
103

Wasu da ake zargin ɓarayi ne sun sace motar ofishin Nuhu Ribadu, mai bawa shugaban ƙasa shawara a fannin tsaro a wani masallacin juma’a dake birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa an ajiye motar a kusa da wani masallacin birnin tarayya Abuja da misalin ƙarfe 1:05, lokacin da jami’an ofishin Nuhu Ribadu suka je yin sallar juma’a.

Tuni dai jami’an rundunar ƴan sandan Abuja suka fara gudanar da binciken wadanda suka sace motar mai ƙirar Toyota Hilux.

Ɗan jarida mai sharhi akan harkokin tsaro Zagazola Makama, ya wallafa a shafin sa na X cewa jami’an ofishin na Ribadu sun iske babu motar a wajen da suka ajiye ta yayin da suka kammala Sallar Juma’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here