An kashe ƙasurgumin ɗan ta’adda da mayaƙa 100 a Katsina

0
73
Sojoji
Sojoji

Jami’an tsaro sun kashe ƙasurgumin ɗan bingida mai suna Gwaska a jihar Katsina tare da wasu mayaƙa 100 a wani harin da sojoji suka kaiwa masu aikata ta’addanci a jihar.

Kwamishinan Tsaro da harkokin Cikin Gida na Jihar, Dr. Nasir Mua’zu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Yace a lokacin harin, jami’an tsaro sun ƙwato bindigogi tare da lalata wasu bindigu masu jigida har guda biyu da bindigogin da aka ƙera a gida biyu da sauran makamai.

Ya bayyana cewa runduna ta 17 ta sojin Nijeriya tare da sojin saman ƙasa ne suka ƙaddamar da hare-haren ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2025 a dabar ɓarayin dajin dake Mununu Bakai da Zango da Jeka Arera da Malali, da kuma Ruwan Godiya duka a cikin ƙananan hukumomin Kankara da Faskari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here