Rundunar ƴan sandan jihar ce ta kama mutumin mai kimanin shekaru 50 a ƙauyen Kurmi Ado, dake ƙaramar hukumar Ganjuwa.
Rundunar ƴan sandan ta ce tana zargin mutumin mai shekara 50 da cewa ya riƙa yi wa ƴar tasa mai shekara 17 fyaɗe, lamarin da ya sa har ta kai ga ɗaukar ciki.
Mai magana da yawun rundunar SP Wakil ya ce bayan samun rahoton zargin rundunar a fara gudanar da bincike tare da kama mutumin.
Kakakin ƴan sandan ya ce a lokacin da ake yi wa magidancin tambayoyi ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikata wa.
BBC ta rawaito cewa SP Wakil ya ƙara da cewa a lokacin da ƴansanda ke yi wa yarinyar tambayoyi ta tabbatar da tuhumar mahaifin nata, tana mai cewa lamarin ya faru ne a lokacin da mahaifiyarta ta yi bulaguro zuwa wajen danginta.