An kama mafarauta ƴan arewa a jihar Edo

0
142

An kama wasu mafarauta ƴan arewa su 4, a jihar Edo, akan zargin su da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Idan za’a iya tunawa a ƴan kwanakin baya ne aka kama wasu mafarauta 16 a Edo tare da ƙone su bisa zargin su da aikata garkuwa da mutane.

Rundunar ƴan sandan jihar ce ta tabbatar da kamen ta bakin kakakin ta CSP Moses Iyamu, inda ya musanta labarin cewa wadanda aka kama ɗin ɓata gari ne.

Mafarautan da aka kama sune Abdulkarim, Mujaheed Garba, Shittu Idris, Jamilu Habibu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here