Babban birnin tarayya Abuja kaɗai ya tattara kuɗin shigar da ya zarce na ɗaukacin jihohin arewa maso yamma a shekarar 2023.
Jihohin arewa maso yammacin Najeriya dai sun ƙunshi Kaduna, Kano, Jigawa, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi.
Wasu alƙaluma daga hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS sun nuna cewa a shekarar 2023, jihohin 7 sun tattara kuɗin shiga na cikin gida da yawan su yakai Naira biliyan 206.23 a daidai lokacin da babban birnin tarayya Abuja ya tattara Naira biliyan 211.10.
Kaduna ta tara Naira biliyan 62.49, sai Kano Naira biliyan 37.38, jihar Jigawa na da Naira biliyan 27.54, Katsina biliyan 26.96, Zamfara biliyan 22.16, Sokoto biliyan 17.96 sai Kebbi tana da Naira biliyan 11.74.