Zulum ya gana da hafsoshin tsaron ƙasa akan farfaɗowar ayyukan ƴan Boko Haram

0
30

Gwamnan Borno ya gana da hafsoshin tsaron ƙasa dangane da farfaɗowar hare haren Boko Haram a jihar sa.

Zulum ya yi ganawar a jiya Alhamis, a birnin tarayya Abuja don tattaunawa da manyan jami’an tsaron akan hanyar da za’a bi domin fatattakar matakan Boko Haram da kuma dakile tasirin da suke dashi a wannan lokaci.

Cikin wadanda aka yi ganawar dasu akwai shugaban sojojin ƙasa Laftanar janar Olufemi Olatubosun Oluyede, da shugaban sojojin ruwa Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla, da shugaban sojojin sama Air Marshal Hasan Bala Abubakar.

Bisa yadda rahotanni suka bayyana a yayin tattaunawar anyi magana akan yadda za’a mayar da hankali wajen inganta aikin soji da bayanan sirri a tsakanin jami’an tsaro da haɗin kai don fuskantar sabbin ƙalubalen rashin tsaron dake shirin sake kunno kai a yankin arewa maso gabas.

A yayin ganawar, Zulum ya samu rakiyar sanatocin Borno, Muhammad Ndume, Tahir Monguno da Kaka Shehu Lawan, sai wasu yan majalisar wakilan jihar da Kwamishinan yaɗa labarai na Borno Farfesa Usman Tar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here