Hukumar dake hasashen yanayi ta ƙasa (NIMET) tace akwai yiwuwar a samu sauyin yanayin daya kunshi ruwan sama da iska mai ƙarfi a sassan Najeriya.
NIMET ta sanar da hakan cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis, wanda tace yanayin zai fara canjawa daga yau juma’a zuwa Lahadi.
Hukumar tace akwai bukatar jihohin kudu su shirya wa fuskantar ambaliya.
Hasashen yace za’a samu mamakon ruwan sama a jihohin Ogun, Oyo, Osun, Lagos, Ondo, Ekiti, Edo da Imo, cikin wannan rana ta juma’a.
Su kuwa yankunan Abuja, Neja, Kwara, Filato, Adamawa, Kaduna zasu samu ruwan sama matsakaici, sai kuma Nasarawa Kogi da Benue zasu samu yayyafi.
Suma jihohin Jigawa, Yobe, Borno da Bauchi zasu fuskanci iska mai ƙarfi.