Mahukuntan Taliban dake mulkin ƙasar Afghanistan sun zartar da hukuncin kisa akan wasu mutane 3, bayan samun su da laifin kisan kai.
An dai zartar musu da hukuncin a bainar jama’a a sassan ƙasar.
An harbe maza biyu a lardin Badghis, yayin da aka harbe mutum ukun a garin zaranj dake lardin Nimroz.
Cikin wata sanarwa da Taliban ta fitar ta ce an samu mutanen uku da laifin kisan kai sannan aka yanke musu hukuncin kisa kamar yadda shari’ar Muslunci ta tanada.
A watan Nuwamban da ya gabata ne aka aiwatar da hukuncin kisa na ƙarshe da aka aiwatar a Afghanistan.