Kwamitin dake yaƙi da masu harkar daba da tabbatar da zaman lafiya da gyara halayyar matasa a jihar Kano, ya bayyana samun nasarar kama bata gari da yawan su yakai 400 a jihar Kano.
Kwamitin ya ce daga cikin waɗanda aka kama, an yankewa kashi 70 cikin 100 a cikin su hukunci.
Rikicin daba dai ya jima yana tayar da hankalin al’ummar Kano, da hakan ke haifar da firgici a zukatan mutane don gujewa abin da kaje yazo, na jiwa al’umma rauni, kwace da sauran su.
A wani lokacin mutane ka iya rasa damar zuwa wasu guraren da hutawa a kofar gidajen su idan dare yayi, baya ga masu kwacen waya, babur, kuɗi da sauran su.
Dr Yusuf Ibrahim Kofar mata shi ne shugaban kwamitin ya yi wa BBC ƙarin bayani, inda ya ce zuwa yanzu sun samu nasarorin da aka daɗe ba a samu ba.
Ya ce, aiki ne babba, amma suna aiki sosai domin shiga lungu da saƙo tare da taimakon jami’an tsaro.
Yace suna da kotun ta fi da gidanka, inda ake yanke hukunci nan take.