An roƙi Tinubu ya saka dokar ta ɓaci a jihar Zamfara

0
48

An nemi shugaban ƙasa Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihar Zamfara saboda taɓarɓarewar sha’anin tsaro.

Wata Kungiyar ƴan arewa mai suna NCAJ ce ta nemi shugaban ya saka dokar.

Kungiyar tace dalilin da ya sa take neman ayyana dokar ta-baci a jihar, shine yadda take zargin gwamnatin Zamfara da hannu a ayyukan hakar ma’adinai.

Cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar Mallam Kabiru Sani Bako, ya fitar a yau juma’a a birnin Kaduna, yace kwace mulki daga hannun gwamnatin Zamfara itace kaɗai hanyar dawo da zaman lafiya a jihar, saboda a cewar sa gwamnatin Zamfara ce ke cin ribar rashin tsaron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here