Tsohon shugaban ƙasa Buhari ya ce kadarar da ya mallaka tun kafin ya hau mulki ba ta ƙaru ba har bayan saukarsa daga mulki a watan Mayun 2023.
Cikin wata sanarwa da kakakin tsohon shugaban, Garba Shehu ya fitar ya ce Buhari ya bayyana haka ne a lokacin ganawa da gwamnonin APC da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Kaduna.
Tsohon shugaban ya shawarci gwamnonin na APC su rungumi aniyar hidimta wa al’umma, yana mai cewa shugabanci cike yake da tarin ƙalubale da kuma dama, kuma haɗa abubuwan biyu ne zai ciyar da ƙasa gaba.
Buhari ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan gwamnonin APC da irin nasarar da ya ce ana samu a jihohinsu.
Tsohon shugaban ya kuma gode wa gwamnatin Tinubu saboda gyara masa gidansa na Kaduna.