Gwamnatin tarayya ta bawa kamfanin China aikin inganta lantarki

0
98
wutar lantarki

Gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniyar dala miliyan 328 da digo 81 da kamfanin China Machinery Engineering Corporation (CMEC) domin inganta wutar lantarki a Najeriya. 

A cewar kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, kwangilar ta shafi aikin injiniyoyi, sayayyar kayan aiki, gine-gine, da kuma samar da kudade don aiwatar da layukan lantarki a karkashin kashi na 1 na shirin samar da wutar lantarki na (PPI). 

A taron rattaba hannu akan yarjejeniyar a Abuja ranar Laraba, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce kamfanin CMEC ne zai gudanar da aikin wutar.

Ya ce wasu daga cikin ayyukan sun hada da gyarawa da gina layukan wuta mai karfin kilovolt 330 (kV) da 132kV.

 Adelabu ya ce an tsara aikin ne domin inganta babban turken lantarki na kasa da kuma hana tabarbarewar aikin wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here