Gwamnatin Kano ta tura jami’ai zuwa Edo akan kisan gillar ƴan farauta

0
36

Gwamnatin Kano ta tura tawaga ta musamman zuwa jihar Edo, don binciken gaskiyar abin da ya faru na kisan mafarauta ƴan asalin Kano.

An kafa kwamitin tawagar karkashin jagorancin mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da mai magana da yawun mataimakin gwamnan Ibrahim Garba Shu’aibu, ya fitar, inda yace kwamitin ya ƙunshi fitattun mutane daga Kano wanda suka haɗar da Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umar, Kwamishinan harkokin addini, shugaban ƙaramar hukumar Bunkure, Kwamishinar mata, kwamishinan ayyuka na musamman da sauran manyan jami’an gwamnatin Kano.

An dai kafa kwamitin don binciken kisan Hausawa mafarauta ƴan asalin jihar Kano su 16 a garin Uromi na jihar Edo, wanda wasu matasa suka aikata mummunan kisan gilla ga Hausawan.

Mataimakin gwamnan Kano, ya bayyana cewa zasu yi bakin kokari wajen tabbatar da adalci ga iyalan waɗanda aka kashe.

 Ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano a yau Alhamis.

Yace babban aikin kwamitin shine bankaɗo gaskiyar abin da ya faru akan kisan, da kuma bayar da shawara akan yadda za’a magance matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here