Gwamnan riƙon ƙwarya na jihar Rivers Ibok Ete Ibas, ya bayar da umurnin daukar sabbin ma’aikata dubu goma a fadin jihar.
Dakataccen gwamnan jihar Siminalaya Fubara, ne ya rushe ɗaukar ma’aikatan wanda tsohon gwamnan Rivers Nyesom Wike, ya kaddamar kafin barin sa mulki.
Fubara, yayi alƙawarin cewa za’a gudanar da sabon shirin ɗaukar ma’aikatan.
Wike dai ya umarci ɗaukar ma’aikatan ne da manufar cike giɓin da ake dashi a tsarin aikin gwamnatin Rivers a wancan lokaci.