Babban Sufeton ‘yan sandan ƙasa Kayode Egbetokun, ya tura rundunar yaki da ta’addanci zuwa jihar Filato saboda tabarbarewar sha’anin tsaro.
Matakin ya biyo bayan wasu hare-hare da kashe-kashe da suka addabi al’umomin jihar a baya bayan nan.
D Hare-haren sun faro a ranar 28 ga watan Maris, 2025, inda sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma ƙone gidajen mutane
Egbetokun wanda ya bayyana faruwar lamarin a matsayin mai matukar tayar da hankali ya umurci mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda mai kula da sashen ayyuka, Kwazhi Dali Yakubu da ya jagoranta tare da daidaita ‘wannan lamari, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar.
Idan za’a iya tunawa dai hare haren da aka kai jihar Filato sun yi sanadin mutuwar mutane 52.