Najeriya ta hana a shigo mata da kayayyakin kasuwancin ƙasar Amurka

0
92

Gwamnatin Amurka ta nuna damuwa kan wasu kayayyakin kasuwancin ta 25 da Najeriya ta hana shiga da su ƙasar, inda Amurka ke cewa hakan na daƙile mata samun riba.

Hukumar kula da harkokin kasuwancin Amurka ce ya bayyana hakan a ranar Litinin cikin wata sanarwar data fitar.

Sanarwar na zuwa bayan da Shugaban ƙasar Donald Trump ya ƙaƙaba wa kayayyakin ƙasashen duniya 60 ƙarin haraji, ciki har da na kashi 14 cikin 100 da ya saka wa Najeriya.

BBC ta rawaito cewa hukumar USTR ta ce cikin kayan da Najeriya ta hana shiga da su ƙasar ta sun shafi noma, da magunguna, da ababen sha, da naman alade, da kayan kiwon kaji.

Masana tattalin arziki na cewa Najeriya ta yi hakan ne saboda ta haɓaka kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida a shekarar 2016.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here