Karyewar farashin ɗanyen man fetur na ƙoƙarin kawo wa Najeriya cikas

0
56

A yanzu haka ana siyar da kowacce ganga ɗaya akan Dala 59, wanda hakan babbar barazana ce ga yanayin samun kuɗin shigar da Najeriya ke tattarawa daga fannin fetur.

Fannin fetur dai shine yafi Kowanne bangare kawo wa Najeriya kuɗin shiga.

Tun da farko Najeriya ta tsara kasafin kudin ta na shekarar 2025, akan cewa kowace gangar mai ɗaya za’a siyar da ita akan Dala 75.

Karyewar farashin nada alaƙa da yadda shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da ƙaƙabawa manyan kasashen duniya haraji akan kayayyakin da suke shigarwa Amurka.

Bayan haka kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur, tace zata kara yawan ɗanyen man da take fitarwa da ganga 411,000, zuwa cikin watan Mayu, wanda hakan ka’iya ƙara rage farashin man.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here