Saudiyya ta saka lokacin da masu Umrah zasu bar ƙasar

0
47

Ma’aikatar aikin Hajj da Umrah ta ƙasa mai tsarki ta sanar da ranar 1 ga watan Zhul Qa’ada, wadda ta zo dai-dai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ya shiga kasar domin yin Umrah zai fice domin komawa gida.

Ma’aikatar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2025.

Cikin wata sanarwa, da aka fitar ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da tayi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe ga masu shiga kasar domin aikin Umrah.

Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a Saudiyya har ya wuce lokacin da aka bayyana, ya saba ka’ida sannan zai fuskanci hukunci.

Sanarwar ta ce duk kamfanin da aka samu da kin bayyana mutanen da suka ki koma wa kasashensu to za a ci tararsu riyal dubu 100.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here