Najeriya da Saudiyya zasu yaƙi fataucin miyagun kwayoyi 

0
35

Kasashen Nigeria da Saudiyya sun sanya hannu akan wata yarjejeniyar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, ta Najeriya NDLEA da takwararta ta Saudiyya GDNC, ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar yaƙi da masu fataucin miyagun ƙwayoyin.

Daga cikin yarjejeniyar akwai musayar bayanai sannan Saudiya za ta bawa NDLEA damar bada horo na hadin gwiwa ga jami’an ta a cibiyar horaswa ta Saudiyya, tare da binciken sirri na hadin gwiwa.

Da yake jawabi bayan sanya hannun, shugaban NDLEA, Birgediya janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya ce Saudiya da Nijeriya sun jima su na kulla ƙawance a fannoni da dama na ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here