Gwamnoni na yiwa shugabannin ƙananun hukumomi barazana akan kuɗin su na gwamnatin tarayya

0
40

Gwamnoni na cigaba da bin hanyoyin dakatar da turawa ƙananun hukumomi kudaden su kai tsaye daga gwamnatin tarayya.

Kimanin watanni 9 kenan da kotun koli ta yanke hukunci kan cewa dole ne ƙananun hukumomin Najeriya 774 su kasance masu cin gashin kansu, da tafiyar harkokin kuɗin su ba tare da sanya hannun Gwamnatocin jihohi ba.

Sai dai har yanzu abin yaci tura, inda ko a kwanakin baya an rawaito cewa gwamnonin sun roki gwamnatin tarayya da ta dakatar da batun aikawa kananan hukumomi kuɗin su kai tsaye.

Wani binciken jaridar Punch, ya nuna cewa wasu daga cikin Gwamnoni na yin barazana ga shugabannin ƙananun hukumomi akan kar su sake su bude asusu a babban bankin kasa CBN wanda dashi za’a yi amfani wajen turawa kowace karamar hukuma nata kason kai tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here