An gabatar da jana’izar mutum shida daga cikin mutane Goma sha uku da lakurawa suka kashe a garin Morai dake mazabar Yola, a karamar hukumar mulki Augie jihar Kebbi.
Lamarin ya faru bayan da ‘yan sa-kai suka yi kokarin hana Lakurawa daukar dabbobin mutanen yankin.
Gwamna Nasir Idris na jihar ta Kebbi a ranar Lahadi ya yi allawadai da harin wanda ya ce ya girgiza shi.