Kungiyar tuntuba ta Arewa ta nemi a biya diyyar wadanda aka kashe a Filato

0
69
Map-of-Plateau-State

Kungiyar tuntuba ta arewa ACF ta bayyana damuwar ta akan yadda ake yiwa mutane kisan gilla a jihar Filato, musamman mata da kananun yara.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar Tukur Muhammad, ya fitar yana mai cewa kungiyar ta nemi gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta baci a guraren da ake samun tashe-tashen hankulan.

:::Gwamnatin tarayya ta haramta ayyukan kungiyar Lakurawa

Ƙungiyar ta kuma yi kira da a Æ™ara Æ™aimi wajen tattara bayanan sirri, sannan a Æ™ara Æ™arfafa jami’an tsaro wajen bibiya tare da kama masu laifi, domin a hukunta waÉ—anda aka samu da laifi.

Haka kuma ACF ta buƙaci a tabbatar da biyan diyya ga wadanda suka rasa ran su, sannan a tallafa wa waɗanda suka jikkata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here