Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar LP a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana jin dadin sa akan yadda rundunar ƴan sandan ƙasa ta janye gayyatar da ta yiwa Sarkin Kano Muhammad Sanusi II.
Tunda farko rundunar ƴan sandan kasa ta gayyaci sarki Sunusi zuwa shalkwatar ta dake Abuja don amsa wasu tambayoyi game da rikicin da aka samu lokacin da ya gudanar da hawan Sallah a ranar 30 ga watan Maris.
Da yake mayar da martani a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Obi ya ce akwai bukatar ayi amfani da maslaha wajen magance duk wani abun daya taso, inda yace haka ne zai kawo zaman lafiya da amincewar jama’a.
Na kuma yabawa yan sanda saboda janye gayyatar da suka yi a lokacin da ya dace, inji Peter Obi
Sannan ya ƙara da cewa idan aka yi la’akari da yanayin tashin hankali a cikin al’umma a yanzu, irin wannan gayyata ba ta da wani amfani, kuma tana iya ƙara tayar da hankali.