Fashewar Gas mai ƙarfi tayi sanadiyar jikkatar mutane 15, ta hanyar jin munanan rauni, biyo bayan faruwar lamarin a yankin Ijora Badia dake karamar hukumar Apapa Iganmu.
Lamarin dai ya faru a yammacin jiya Lahadi.
Fashewar ta faru da misalin karfe 4:10, na yamma lokacin da wata tukunyar gas mai nauyin kilo 25 tayi bindiga, a wani shagon siyar da gas.
Shago ya kasance a jikin wani gida mai mazaunin mutane 15, da kuma shaguna 7.
Shugabar hukumar bada agajin gaggawa akan faruwar gobara Margaret Adeseye, ta tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Lahadi.
Ta kuma ɗora alhakin faruwar fashewar Gas din akan rashin bayar da kulawa yayin ma’amala da shi.