Adadin bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru zuwa Naira triliyan 144.67, wanda yayi daidai da dala biliyan 94.23.
An samu ƙarin bashin a daidai lokacin da ake kyautata zaton sake samun karuwar bashin zuwa Naira triliyan 157, zuwa karshen wannan shekara ta 2025.
Hakan ya faru sakamakon cewa gwamnatin tarayya na shirin cike giɓin kasafin kuɗin wannan shekara ta hanyar ciyo bashin Naira triliyan 13.