Najeriya tayi kuskuren barin ƙungiyar Boko Haram tayi ƙarfi—Gwamnan Filato

0
22

Gwamna jihar Filato Caleb Mutfwang, ya nuna takaici akan cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga suka yi ƙarfi.

Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro na ƙasa cikakkiya.

Da yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da jiragen yaƙi marasa matuki da bama-baman da aka ƙera a Najeriya, wanda kamfanin Briech UAS ya samar, Mutfwang ya buƙaci haɗin gwiwa da kamfanonin fasahar tsaro na cikin gida don magance matsalolin tsaron.

Gwamnan yace dole ne a tabbatar da cewa babu wata ƙungiya da ke iya ƙalubalantar hukumomin tsaron kasar nan.

Ya kuma yaba wa sojoji kan ƙoƙarinsu na inganta tsaro a Jihar Filato.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here