Bankin duniya ya sake bawa Najeriya sabon bashin Dala biliyan 1.13.
Bankin ne ya sanar da hakan a shafin sa intanet, inda yace ya amincewa bukatun da Najeriya ta shigar masa guda 3, tun a watan Maris, wanda za’a yi amfani da kuÉ—in wajen inganta harkokin ilmi, inganta samar da abinci mai gina jiki, da cigaban muhalli.
Bankin yace za’a yi amfani da dala miliyan 80 a fannin haÉ“É“aka samar da abinci mai gina jiki sai dala miliyan 552, na inganta ilimi, sai kuma dala miliyan 500, da za’a yi amfani da ita wajen inganta tattalin arziki da cigaban al’umma.
Wannan shine ya nuna cewa daga farkon shekarar 2025 zuwa yanzu bankin duniya ya bawa Najeriya bashin Dala biliyan 2.2.