Abba Bichi ya miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano

0
36

Ɗan majalisar wakilai na ƙaramar hukumar Bichi Abubakar Kabir Abubakar, ya miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi, wanda ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.

Abubakar Kabir Abubakar, ya miƙa saƙon ta’aziyyar tasa cikin wata sanarwar daya sanyawa hannu.

Yace a madadin sa da ɗaukacin al’ummar da yake wakilta sun yi alhanin rasuwar Galadiman wanda tuni aka yi jana’izar da kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Abba Bichi, ya bayyana kaɗuwar sa da jin labarin rasuwar Galadiman Kano, wanda yayi rayuwa cikin kwanciyar hankali da ya kamata ayi koyi da shi.

Sanarwar tace mutanen Bichi na ci gaba da jin marigayi Galadiman Kano a matsayin nasu, kamar yadda aka haife shi a Bichi a lokacin da mahaifinsa, Marigayi Sarki Muhammad Sanusi na ɗaya, yake a matsayin Hakimin Bichi.

Abba Bichi, ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyar ga shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas, wanda ya kasance ɗa a wajen Galadiman. Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta masa ya sanya shi a aljannar Firdaus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here