Ƴan adawar siyasa ne suka ƙirƙiro cewa na yanke jiki na faɗi—Wike

0
31

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta masu cewa ya yanke jiki ya faɗi warwas a makon da ya gabata.

Wike ya karyata labarin a yau Alhamis lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Vanguard ta rawaito Wike na cewa waɗannan rahotannin ƙirƙirarru ne daga wasu mutane da ke ƙoƙarin cimma burinsu na siyasa.

Wike ya yi wannan bayani bayan ya kammala duba wasu ayyuka guda huɗu da ake ci gaba da aiwatarwa a birnin tarayya Abuja ciki har da aikin Cibiyar Taro ta Ƙasa (ICC).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here