Shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya kori shugaban kamfanin mai na ƙasa NNPCL Mele Kyari daga mukaminsa, tare rushe mambobin hukumar gudanarwar Kamfanin karkashin jagorancin Pius Akinyelure.
Tinubu ya kuma naɗa Bayo Ojulari Bashir, a matsayin sabon shugaban kamfanin bayan korar Mele Kyari.
Mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan da sanyin safiyar Laraba, a shafin sa na X.
Tun da farko tsohon shugaban Najeriya Buhari, shine ya naɗa Kyari a matsayin shugaban NNPCL, wanda Tinubu ya ƙara naɗa shi a shekarar 2023.