Ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano na jam’iyar APC a zaɓen shekarar 2023, Alhaji Murtala Sule Garo, ya miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi, daya rasu a daren jiya Talata.
Abbas Sunusi, shine babban ɗan majalisar masarautar Kano da yafi kowa daɗewa a duniya, inda ya rasu yana da shekaru 92 a duniya.
Garo, ya miƙa saƙon ta’aziyyar cikin wata sanarwar daya sanyawa hannu a yau Laraba. Ya kuma bayyana Marigayin a matsayin dattijon da ya bayar da gudummawa wajen cigaban Kano, da masarautar Kano.
Yace rashin Galadiman Kano, ba na iya ahalin sa bane, abune daya shafi masarautar Kano da al’ummar jihar baki ɗaya saboda ya bayar da gudummawa a fannin shugabanci.
Tsohon Kwamishinan kananan hukumomin Kano, ya kuma yi addu’ar samun rahama ga Alhaji Abbas Sunusi, tare da neman Allah ya bawa iyalan sa hakurik jure rashin.
Garo, ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyar ga shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas, yana mai rokon Allah ya sanya mahaifin nasa a aljannar Firdaus.
Shi dai marigayi Galadiman Kano an haife shi a shekarar 1933, ya kuma rike mukamin wamban Kano, daga bisani Sarkin Kano Muhammad Sanusi II, ya mayar da shi Galadima a shekarar 2014.