Turmutsutsu a filin idi na Gombe a lokacin bukukuwan Sallah ƙarama ya yi sanadin mutuwar mutane biyu tare da jikkata 20.
Lamarin ya faru da misalin karfe 10:45 na safiyar Lahadi, bayan kammala sallar wadda gwamnan jihar Inuwa Yahaya da Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar suka halarta.
Binciken Leadership ya nuna cewa hakan ya faru ne a lokacin da jama’a ke kokarin ficewa daga filin idi, lamarin da ya haddasa turereniya, musamman a bakin kofar fita.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane 22 ne lamarin ya shafa, ciki har da yara biyu da suka rasu, Aisha Salisu Ahmed mai shekara hudu da rabi, da Maryam Abdullahi Gwani mai shekara huɗu.
Kakakin ‘yan sandan jihar Gombe, Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa hakan ya samo asali daga cunkoson jama’a da zafi mai tsanani.
Ya kara da cewa an gaggauta kai wadanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban domin kulawa da lafiyarsu