Gwamnan Edo ya kawo ziyarar jaje jihar Kano

0
62

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kawo ziyarar jaje ga gwamnatin jihar Kano da iyalan mafarauta 16 da ɓatagari su ka kone a garin Uromi na jihar ta Edo.

Da ya ke jawabi a gidan gwamnati, Okpebholo ya nuna kaɗuwa bisa lamarin, inda ya tabbatar da cewa 14 daga waɗanda su ka aikata kisan sun shiga hannu kuma za a tabbatar an yi wa iyalan wadanda aka kashe adalci.

Shi ma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga gwamnan na Edo da ya tabbatar da an hukunta waɗanda ake zargi. 

Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bayyana fuskoki da sunayen mutane da aka kama kan kisan gillar, inda ya bukaci gwamnan Edo ya tabbatar an biya diyya ga iyalan mamatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here