Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, yace yan Najeriya ba zasu yi nadamar zaɓen Tinubu a matsayin shugaban ƙasa ba, bayan kammala wa’adin mulkin Najeriya na farko.
Ganduje ya bayyana hakan cikin saƙon barka da Sallah daya aikewa musulman Nijeriya, a ranar Lahadi, ta hannun mai magana da yawun sa Edwin Olofu, inda ya roke su dasu cigaba da yiwa Tinubu addu’ar samun nasara.
Ya bukaci mabiya addinin Musulunci da su ci gaba da rayuwa bisa kyawawan halaye na ibada, sadaukarwa, da tausayi da darasin da Ramadan ke koyarwa, tare da nuna soyayya da jin ƙai ga juna, musamman ga marasa ƙarfi.