Ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa NBA reshen ƙaramar hukumar Ungogo dake jihar Kano tayi ala wadai da kisan gillar da aka yiwa Hausawa yan asalin Kano a jihar Edo, lokacin da suke hanyar komowa gida daga kudu.
Ƙungiyar tace kisan ya saɓawa yancin da kowanne ɗan ƙasa yake da shi wajen gudanar da rayuwa yadda yake so.
Shugaban kungiyar Ahmad A. Gwadabe ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar daya fitar, yana mai cewa suna bukatar gwamnatin Edo da jami’an tsaro du dauki tsauraran matakai akan waɗanda aka samu da hannu a laifin kisan.
Har ila yau NBA ta nemi a biya diyya ga iyalan mutanen su 16, da kuma hana sake samun irin wannan abu a nan gaba.