Rashin zuwan Wike wajen murnar cikar Tinubu shekaru 73 a duniya, ya haifar da shakku dangane da batun lafiyar sa.
Wasu rahotanni marasa tabbas sun bayyana cewa Wike ya faÉ—i a lokacin gudanar da wani taro a birnin tarayya Abuja.
Sai dai wani hadimin sa Lere Olayinka, yace ministan na Abuja Nyesom Wike yana cikin ƙoshin lafiya.
A jiya Asabar ne aka yi shagalin cikar Tinubu shekaru 73 a duniya, wanda manyan jami’an gwamnatin tarayya suka halarta amma ba’a hangi Wike ba, duk da irin amincin dake tsakanin sa da shugaban Æ™asa Tinubu.
Wannan abu ya haifar da shakku akan cewa wane dalili ne ya hana ministan halartar taron mai muhimmanci.