Saura ƙiris na janye takarar shugaban ƙasa—Tinubu

0
46

Shugaba Tinubu, yace saura kaɗan ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban Najeriya kafin zaɓen shekarar 2023.

Yace yanayin matsalolin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki ne ya sanya shi fara tunanin janye neman shugabancin gabanin zaɓen 2023.

Tinubu ya bayyana hakan a jiya Asabar lokacin da aka shirya masa liyafar murnar cikar sa shekaru 73 a duniya, wanda taron ya ƙunshi manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya da iyalan shugaban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here