Ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano na jam’iyar APC a shekarar 2023, Alhaji Murtala Sule Garo, ya taya ƴan uwa musulmi murnar zagayowar ƙaramar Sallah, tare da roƙon al’umma su cigaba da aikata kyawawan halayen da suka koya a watan Ramadan.
Alhaji Murtala, ya bayyana hakan cikin saƙon murnar Sallar daya fitar a daren Asabar, inda yace akwai bukatar a cigaba da bautawa Allah kamar yadda aka riƙa yi a watan Ramadan.
Ya kuma nemi a yi amfani da lokutan bukukuwan Sallar don yiwa jihar Kano da Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.